Shirin ya ce ya damu matuka da ta'azarar rikicin na Sebha, inda a kalla fararen hula 6 suka mutu yayin da wasu 9 suka jikkata.
Ya kara da cewa ana kai hari kan asibitin birnin akai akai, yana mai cewa dole ne a dakatar da kai hari kan al'umma.
An shafe kwanaki ana kwabza rikicin kibilanci a birnin Sahba dake da nisan kilomita 800 daga kudu maso yammacin birnin Tripoli.
Birnin na fuskantar rashin tsaro saboda karuwar laifufuka da sace sace da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi tare kuma da rikicin kabilanci. (Fa'iza Mustapha)