in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta bukaci al'ummomin kasashen waje su yi yaki da kwararar bakin haure
2018-02-23 10:22:41 cri
Kasar Libya ta yi kira ga kasashen duniya, su taimaka wajen warware matsalar kwararar bakin haure da ta addabi kasar dake fama da yaki.

Ministan harkokin wajen Gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya Mohammed Sayala ne ya yi kiran, yayin wani taro na kwamitoci 3 na kasashen waje kan kwararar bakin haure a Libya, wanda ya samu halartar Jami'an Tarayyar Afrika da takwararta ta Turai da kuma MDD.

Manufar taron ita ce, tattauna hanyoyin taimakawa bakin haure dake watangarari a Libya, ta yadda za a mayar da su kasashensu na asali.

Mohammaed Sayala ya ce ya kamata kasashen Turai su taimaka su samarwa Libya wani tsari ta na'ura, domin bibiya da tsaron iyakokinta, sannan su gudanar da ayyukan raya kasa a kasashen bakin hauren dan rage kwarararsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China