in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin kawance tsakanin AU da EU da MDD na kokarin taimakawa 'yan ciranin Afrika dake watangarari a Libya
2018-03-30 10:34:59 cri
Shirin kawance na Tarayyar Afrika AU da Tarayyar Turai EU da kuma MDD, na kokarin taimakawa 'yan ciranin Afrika dake watangaririya a Libya, yayin da suke kokarin datse hanyoyin safara da fasa kaurin bil adama

Yayin da suke kammala taron shirin jiya Alhamis a birnin Addis Ababa na Habasha, kwamishinar AU mai kula da harkokin al'umma Amira Elfadil, ta shaidawa wani taron manema labarai cewa, an samu ingantuwar yanayi a cibiyoyin tsugunar da 'yan cirani dake karkashin ikon gwamnati.

Kwamishinar wadda kuma ita ce wakiliyar AU ta musammam a Libya, ta bayyana damuwar cewa, har yanzu yanayin da 'yan cirani ke ciki a Libya na bukatar kula sosai, domin shirin kawancen 'yan cirani dake cibiyoyin tsugunar da su mallakar Gwamnati kadai za su iya taimakawa, ban da wadanda ke sauran cibiyoyi masu zaman kansu da wadanda ke karkashin 'yan tawaye.

Jami'ar ta ce shirin na aikin mayar da 'yan ciranin kasashensu na asali ko kuma kasashen da suke zama. A cewarta, shirin kawancen ya mayar da sama da 'yan cirani 16,000 kasashensu daga Libya, kuma adadin wadanda ke cibiyoyin tsugunar da 'yan cirani mallakar gwamnati, ya ragu daga 20,000 a watan Nuwamban bara, zuwa kimanin 3,400 yayin ziyarar karshe da ta kai kasar cikin watan Fabrerun bana.

Bugu da kari, ta ce akwai kokarin da ake na shigar da kwamitin tattara bayanan sirri da tabbatar da tsaro na Afrika, wajen wargaza laifukan da ake aikatawa a Libya da sauran kasashe makwbta dake amfana daga halin ni 'yasu da yan cirani ke ciki, wadanda suka hada da safara da fasa kaurin 'yan cirani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China