in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadar kasar Sin a Nijeriya ya ce akwai alaka ta musammam tsakanin kasashen biyu
2018-03-21 11:34:28 cri
Jakadan kasar Sin a Nijeriya Zhou Pingjian, ya ce Sin da Nijeriya, kasashe ne masu yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyoyinsu, kana akwai alaka ta musamman a tsakaninsu.

Jakada Zhou Pingjian, ya bayyana hakan ne jiya, yayin bikin mika tallafin karatu ga dalibai 47 na jami'ar Jos ta jihar Plateau dake yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Ya ce manufar tallafin ita ce, kara karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu. Yana mai cewa zai kara inganta aminci da hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da Nijeriya.

Jakadan ya yi alkawarin duba yuwar kara tallafin ga dalibai mabukata da wasu tallafin ga daliban da suka kammala karatun digiri domin su bunkasa ingancin ilimi a jami'ar.

Ya kuma kara da shawartar Nijeriya ta bada muhimmanci ga harkar ilimi ta yadda matasa za su samu ilimi da damar raya kasar.

Ya ce babu wata kasa da za ta ci gaba ko ta kasance cikin farin ciki matukar matasanta ba sa cikin farin ciki. Haka zalika babu wata kasa da za ta bunkasa muddun ba ta cikakken amfani da basirar matasanta.

Zhou wanda ya bayyana Sin da Nijeriya a matsayin kasashe masu tasowa, ya ce kasar Sin ta dukufa wajen fatattakar talauci da kashi dari bisa dari ya zuwa shekarar 2020. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China