in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci shugaban Najeriya ya kawo karshen hare haren makiyaya
2018-03-21 10:39:27 cri
An bukaci shugaba Najeriya Muhammadu Buhari ya kawo karshen hare haren makiyaya, da masu yin garkuwa da mutane da sauran muggun ayyuka a shiyyar arewacin kasar da ma sauran wasu sassa na kasar.

Da yake jawabi a birnin Kaduna na tsakiyar arewacin kasar, Ibrahim Coomasie, shugaban kungiyar tuntuba ta dattawan arewa wato (ACF) ya ce ya kamata gwamnati ta yi dukkan abin da ya dace domin kawo karshen yawan kashe-kashen rayuka, da masu yin garkuwa da mutane, da ma sauran munanan laifuka a kasar.

Yawan kashe-kashen da makiyaya ke kaddamarwa, da yin garkuwa da mutane, musamman sace 'yan mata 110 na makaranta sakandaren kimiyya ta 'yan mata ta Dapchi, a jahar Yobe, da sauran muggan laifuka yana haska wani mummunan yanayi da yankin ke fuskanta, tsohon babban jami'in hukumar 'yan sandan ya bayyana hakan ne ga manema labarai.

Coomasie ya ce, kungiyar ACF ta damu matuka game da yawan kashe-kashen da ake fama da shi a shiyyar arewacin kasar.

Shugaban na ACF ya bukaci shugabannin arewa da su hada kansu don yin aiki tare da nufin ceto yankin daga wadannan munanan ayyukan dake neman zubar da kimar yankin arewacin kasar.

Tsohon jami'in ya bukaci gwamnatin shugaba Buhari da ta yi dukkan abin da ya kamata wajen kawo karshen kashe-kashen da yin garkuwa da mutane musamman ma mata da kananan yara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China