Girke na'urorin THAAD ya cutar da alakar cinikayya tsakanin Sin da Koriya ta kudu, in ji wani jami'i
Mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya ce girke na'urorin kandagarkin makamai masu linzami nau'in THAAD a kasar Koriya ta kudu, ya haifar da illa ta fannin hada hadar cinikayya tsakanin bangaren Sin da na Koriya ta kudun.
Mr. Gao Feng ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar. Ya ce Sin na fatan Koriya ta kudu za ta martaba manyan muradun kasar Sin, da abubuwan da take mai da hankali a kansu, ta kuma fara daukar matakan warware sabani a fannin cikin hanzari. (Saminu Hassan)