in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta amince da kudurin da Sin ta gabatar game da kare hakkin bil Adama
2018-03-27 19:07:31 cri

Hukumar kare 'yancin bil adama ta MDD, ta amince da wani kuduri da kasar Sin ta gabatar game da kare hakkin bil Adama, wanda ke kunshe da kira ga kasashen duniya, da su hada kai da juna wajen bunkasa hanyoyin cimma moriyar juna.

An dai amince da kudurin mai taken "bunkasa hadin gwiwa domin cimma moriyar juna a fannin kare hakkokin bil Adama" ne, a zaman da mambobin hukumar suka yi na ranar Jumma'a.

Kudurin ya fayyace muhimmancin habaka alakar kasashe daban daban ta hanyar martaba juna, da daidaito, da adalci tare da cimma moriya tare, a wani mataki na gina al'umma da ke iya samun makomar moriya guda, wadda kuma sassan ta ke iya cin gajiyar kariya ta hakkokin su.

A daya hannun kuma, kudurin ya yi kira ga kasashen duniya da su karfafa tallafin kwarewa da sanin makamar aiki da suke bayarwa ta hanyar cin moriyar juna, a duk lokacin da aka bukaci hakan, kuma gwargwadon muhimman bukatun kasashen da lamarin ya shafa.

Kaza lika ya jaddada bukatar da ake da ita, ta ganin dukkanin ayyukan hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD sun kasance bisa doka, da daidaito, da bin tsari na gaskiya ba tare da nuna son kai ba. Har ila yau a rika tattaunawa tsakanin kasashen duniya, tare da hada kai da juna domin bunkasawa, da kuma kare dukkanin hakkokin bil Adama, da na ayyukan fararen hula, da harkokin siyasa da na al'adu, wadanda suka kunshi ikon samar da damammaki na ci gaba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China