in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da nahiyar Afrika na neman tabbatar da dorewar dangantakarsu
2017-11-28 09:50:18 cri
An bude taro karo na 2 kan harkokin zuba jari tsakanin nahiyar Afrika da kasar Sin jiya Litinin a birnin Marrakech na kasar Morocco.

Taron wanda ya ja hankalin manyan shugabannin kasuwanci na kasar Sin da nahiyar Afrika har 500, na da nufin tattauna hanyoyin saukaka kasuwanci tsakanin manyan masu ruwa da tsaki kan harkokin cinikayya da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, domin samar da dangantaka mai dorewa da dimbin alfanu, musamman a bangaren raya masana'antu.

Taron da za a shafe yini 2 ana yi, zai tattauna tare da muhawara kan matsalolin kudi ga tattalin arzikin Afrika da kuma yadda za a mayar da nahiyar wani dandali na raya ayyukkan masana'antu.

Baya ga taron, za kuma a gudanar da wani taron bitar da zai bada damar fahimtar manufofin tattalin arzikin kasar Sin da na Afrika tare da yanayin gudanar da ayyuka.

Kasar Sin ita ce muhimmiyar abokiyar huldar kasuwanci ga nahiyar Afrika, inda ta zuba sama da dala biliyan 122 cikin harkokin cinikayya tare da jarin kai tsaye da ba na ruwan kudi ba da ya kai dala biliyan 2.5 a nahiyar a shekarar 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China