in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin hankali ya raba mutane 5,000 da muhallansu a arewacin Burkina Faso a watan Janairu
2018-03-28 11:01:28 cri
Kimanin mutane 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a lardin Soum dake arewacin kasar Burkina Faso a watan Janairun wannan shekara, biyowa bayan tashin hankalin dakaru masu dauke da makamai, wata majiyar hukumar bada agaji ce ta sanar a jiya Talata a Ouagadougou babban birnin kasar.

Hukumar agaji ta ICRC ta sanar da hakan ne bayan da ta samu damar kai tallafin kayan abinci ga mutanen da tashin hankalin ya raba su da matsugunansu, inda hukumar ta ce, yanayin rayuwa da karancin kayayyakin kiwon lafiya ya yi matukar tsananta a yankin.

Idrissa Savadogo, wani jami'in hukumar ta ICRC, wanda yana daya daga cikin wadanda suka kai dauki ga mutanen ya bayyana cewe, magidantan da tashin hankalin ya tarwatsa suna musayar takardun shaidar samar musu da tallafi wajen sayar da su don samun abin da za su ci.

Christian Munezero, shugaban tawagar bada agaji ta ICRC dake aiki a Burkina Faso ya ce, babban burin da suka sanya gabansu shi ne, samarwa mutane damar kiwon lafiya ta hanyar yin hadin gwiwa da hukumar bada agaji ta Red-Cross da sauran hukumomin kasar ta Burkina Faso.

Ya kara da cewa, babban abin da suke fargaba a yanzu shi ne, sauyin yanayin da za'a iya samu tsakanin watan Yuni zuwa Agusta. Mai yiwuwa ne a fuskanci matsalar fari da matsalar tabarbarewar tsaro a wadannan yankunan, in ji shi.

Arewacin kasar Burkina Faso yana daya daga cikin yankunan da suka fi fama da talauci a cikin kasar, kuma yankin ya jima yana fama da matsalar hare haren ta'addanci tun daga shekarar 2015. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China