Mista Guterres ya ce, babu wata takamammiyar hujja na aikata irin wadannan abubuwa na cin zarafin bil adama. Ya jaddada aniyar MDD wajen tallafawa Burkina Faso a kokarinta na yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.
Mai magana da yawun sakatare janar din Farhan Haq, ya ce, sakataren ya nanata aniyarsa ga kasashen G5 na yankin Sahel, sakamakon kalubalolin tsaro da suke fuskanta ta yadda za'a taimaka musu wajen samun dauwamamman zaman lafiya da cigaban yankin.
Kasar Faransa da wasu kasashen Afrika 5 da suka hada da Burkina Faso, Chad, Mali, Mauritania da Nijer, a watan da ya wuce suka cimma matsaya na kaddamar da runduna ta musamman mai yaki da 'yan tada kayar baya masu tsattsauran ra'ayi a yankin Sahel. (Ahmad)