Majiyoyi na cewa, kura na tashi sama sakamakon abubuwan da suka fashe. Haka kuma an ji karar harhe-harbe a kusa da ofsihin jakadancin kasar Faransa dake birnin Ouagadougou. Jama'a dai na arcewa ta ko'ina don neman tsira da rayukansu.
Rundunar 'yan sandan Burkina Faso ta tabbatar da cewa, hari ne na ta'addanci, kuma an killace wurin da aka kai wannan hari. (Ibrahim)