in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Morocco ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a Burkina Faso
2018-03-06 10:30:36 cri
Sarkin Morocco Mohammed VI, ya yi Allah wadai da abin da ya kira harin ta'addanci na matsorata a Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso.

A sakon ta'aziyyar da ya aikewa shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, sarki Muhammad ya nuna cikakken goyon bayansa da kuma nuna alhininsa ga kasar sakamakon ayyukan abin takaici na harin ta'addancin da aka kaddamar a kasar.

Ya nanata cewa, wadannan hare haren ta'addancin ana kaddamar da su ne da nufin wargaza zaman lafiyar da yanayin tsaron kasar Burkina Faso da ma yankin Sahel-Saharar Afrika.

A kalla mutane 16 ne aka hallaka kana wasu 80 suka jikkata a harin da aka kaddamar a ranar Juma'ar da ta gabata, inda aka so kai harin a ofishin jakadancin kasar Faransa da hedkwatar sojojin kasar ta Burkina Faso. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China