Rundunar 'yan sanda Burkina Faso ta tabbatar da aukuwar harin da rahotanni suka ce an kai wa ofishin jakadancin Faransa dake Ouagadougou da kuma hedkwatar rundunar sojin kasar.
Mutane sama da 10 ne suka mutu, ciki har da mahara biyu da wasu jami'an tsaro.
Wata sanarwar da AU ta fitar, ta ce shugaban hukumar kula da ayyukanta Moussa Faki Mahamat, ya ce tarayyar ta na tare da al'umma da gwamnatin Burkina Faso a wannan mayuwacin lokaci.
A nasa bangaren, cikin wata nsanarwa da ya fitar, ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian, ya tabbatar da harin da aka kai ofishin jakadancin kasarsa dake birnin Ouagadougou.
Ministan ya ce jami'an tsaron kasar da taimakon jami'an tsaron ofishin jakadancin, sun tunkari maharan inda suka rage ta'adin harin. (Fa'iza Mustapha)