Baje kolin wanda shi ne irinsa na farko da aka taba yi a Hedkwatar majalisar, ya kunshi hotuna 70 da gajerun hotunan bidiyo 15, wadanda ke bayyana irin nasarorin da kasar Sin ta samu.
Wadanda suka yi kallon baje kolin sun hada da Jakadu da manyan jami'an diflomasiyya da jami'ai daga kasashe da hukumomin daban-daban tare da daruruwan wakilai dake halartar taro na 36 na hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD. (Fa'iza Mustapha)