A jiya Talata ne, hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD ta yi kiran da a samar da yanayin tattaunawa da ya dace domin tafiyar da harkokin hukumar yadda ya kamata.
Shugaban hukumar Joaquin Alexander Maza Martelli wanda ya yi wannan kiran yayin da yake jawabi a zaman hukumar karo na 35 a hedkwatarta dake birnin Geneve, ya kuma tunatar da cewa, hukumar za ta bi ba'asin dukkan laifukan take hakkin bil-Adama da aka gabatar mata.
Shi ma a nasa jawabin shugaba Tabare Vazquez na kasar Uruguay, ya bayyana cewa, wajibi ne dukkan kasashe su amince, su ba da goyon baya kana su shiga a dama da su a harkokin hukumar ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna.(Ibrahim)