in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya nuna damuwa kan rashin sasantawa game da madatsar ruwan Habasha
2018-01-19 09:40:22 cri
Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar ya bayyana damuwa matuka game da rashin cimma tudun dafawa a tattaunawar da ake yi game da aikin gina babbar madatsar ruwan kasar Habasha.

Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da suka shirya da firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn, ya jaddada bukatar ganin an kawo karshen abubuwan dake hana ruwa gudu a tattaunawar sassan biyu game da aikin gina madatsar ruwan. Ya ce ya fahimci manufofin raya kasa da Habashan ke fatan cimmawa a wannan aiki.

Sai dai ya ce, bai kamata aikin gina madatsar ruwan ya kawo illa ga muradun kasarsa ko kason ruwan da Masar din take samu daga kogon Nilu ba. Ya ce, duk da cewa, a wani bangaren a ra'ayinsu ya zo daya shi da firaministan Habasha, zabi ya rage ga kasashen Habasha da Sudan su nazarci shirin da Masar din ke yi na gayyato bankin duniya domin shiga tsakani kan wannan batu.

A nasa bangare firaminista Desalegn ya nanata cewa, madatsar ruwan ba za ta cutar da Masar ba, sai ma ta kara ba da gudummawa ga ci gaban kasashen da kogin Nilu ya ratsa ta cikinsu, musamman kasashen Masar da Sudan.

Dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen Habasha da Masar dai tana da allaka da kogin Nuli wanda ya tasho daga Habasha, kuma kasashen Habashan da Sudan da Masar ke cin gajiyarsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China