Shirin bada horo na mako guda, an tsara shi ne da nufin tallafawa iyaye da yara 'yan makaranta wadanda rikicin 'yan ta da kayar baya ya shafa.
Shugaban kwamitin ba da tallafi na ofishin shugaban kasa a shiyyar arewa maso gabas (PCNI) Theophilus Danjuma, ya ce wannan shirin ya zama dole a kaddamar da shi sakamakon matsalar koma bayan da yankin ya fada ciki musamman ta fuskar ilmi da tattalin arziki. (Ahmad Fagam)