in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kafa cibiyar bunkasa fasahar kirkire kirkire
2018-03-21 10:29:28 cri
A ranar Talata gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wata cibiya da nufin bunkasa fasahar kirkire kirkire a kasar.

Cibiyar bunkasa fasahar zamanin, wanda hukumar kula da kimiyya da fasahar kere-kere ta kafa, an kafata ne da nufin taimakawa fannin kananan sana'o'i, da masu gudanar da bincike, da kuma ba da dama ga masu kirkire-kirkire samun damar da suke bukata wajen bunkasa fannin kirkire-kirkire ta yadda zai bunkasa cikin sauri da kuma bayar da dama wajen sayar da fasahohin zamani da ake samarwa a cikin gida, kamar yadda ministan kimiyya da fasahar Najeriyar, Ogbonnaya Onu ya bayyana.

Jami'in ya ce, sabuwar cibiyar fasahar, an kafa ta ne a Abuja, babban birnin tarayyar, za ta baiwa 'yan Najeriyar sabbin damarmmaki wadanda za su taimaka wajen ciyar da kasar gaba, daga matsayin kasa mai tarin albarkatu zuwa kasar dake amfani da ilmi da kuma kirkire kirkire wajen ciyar da tattalin arzikinta gaba.

Ministan ya kara da cewa, idan aka baiwa fannin kirkire kirkire gagarumin muhimmanci, kuma aka zurfafa aiwatar da sakamakon da aka samu daga binciken aka sarrafa su zuwa mataki na samar da kayayyaki da ayyukan hidima, za'a iya sake samar da wata al'umma mai matsakaicin yanayi, kuma darajar kudin kasar wato Naira zai kara yin sama, kana zai samarwa kasar kyakkyawar makoma a nan gaba domin amfanin al'ummomi masu zuwa a nan gaba.

Hukumomin Najeriya sun yi amanna cewa bisa irin dunbun albarkatun da Allah ya huwacewa kasar kuma a matsayinta na wata babbar kasuwa mafi girma a Afrika, Najeriyar tana da karfin da za ta samar da sabbin hanyoyi wadanda za su taimakawa kasar fadada tattalin arzikinta, ta hanya mai dorewa, musamman ta hanyar karfafawa 'yan kasar gwiwa wajen kirkiro fasahohin zamani daga basirar da 'yan kasar keda ita. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China