in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan kasar Sin ya bukaci a karfafa alaka tsakanin Sin da bankin duniya
2018-03-26 19:51:03 cri
A yau Litinin mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng, ya bukaci karfafa alaka tsakanin Sin da bankin duniya, yayin da yake zantawa da babbar jami'ar babban bankin duniya Kristalina Georgieva.

Mr. Han ya jinjinawa gudummawar da bankin duniya ke baiwa kasar Sin a fannin yaki da fatara, da kare muhalli da kuma bunkasa kirkire kirkire. Ya ce sauran fannoni da ke bukatar hadin gwiwar sassan biyu sun hada da raya karkara, da kyautata muhallin halittu, da shawarar nan ta ziri daya da hanya daya.

Kaza lika ya kara da cewa, Sin na dora muhimmanci matuka ga batun kyautata muhallin gudanar da cinikayya, tana kuma kara himma a wannan fanni.

A na ta bangare Georgieva, wadda ke halartar taron samar da ci gaba na kasar Sin na bana, ta jinjinawa kwazon Sin tun bayan fara gudanar da gyare gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen ketare cikin kusan shekaru 40 da suka gabata.

Ta ce Sin ta yi rawar gani wajen tallafawa bankin duniya, da manufofin yaki da talauci na duniya. Daga nan sai ta bayyana burin bankin na duniya, wajen hadin gwiwar cimma nasarar shawarar ziri daya da hanya daya, da sauran hanyoyin kyautata hada hadar cinikayya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China