in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban bankin duniya ya ce yunkurin Sin na rage talauci muhimmin tarihi ne
2017-10-13 12:48:09 cri

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, ya ce kokarin kasar Sin na taimakawa wajen fitar da mutane miliyan 800 daga kangin talauci muhimmin tarihi ne.

Jim Yong Kim, yayin wani taron manema labarai domin bude taron shekara-shekara na asusun ba da lamuni na duniya da bankin duniya, ya ce, yunkurin wani babban al'amari ne ga tarihin dan Adam.

Ya ce, da samuwar tsarin tattalin arzikin kasar Sin da shigarsa cikin kasuwar duniya, kasar ta fitar da mutane sama da miliyan 800 daga talauci.

Shugaban ya kara da cewa, da matsayin kasar Sin na babbar mai ba da gudummuwa ga ci gaban da ake samu na rage talauci a duniya, adadin mutane da ke cikin matsanancin talauci ya ragu zuwa kasa da kaso 10 daga kaso 40.

Har ila yau, ya ce darussan da aka koya daga aiki a kasar Sin da kuma tabbacin fitar da mutane miliyan 800 daga talauci da kasar ta yi, abubuwa ne da za su taimakawa kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga.

A cewarsa, bankin duniya zai ci gaba da aiki da kasar Sin a fannonin da suka hada da yi wa tsarin kiwon lafiya garambawul. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China