in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da bankin duniya sun fitar da rahoto game da magance rikici a duniya
2018-03-15 10:44:12 cri

MDD da bankin duniya sun fidda wani rahoton hadin gwiwa game da matakan da za su taimaka wajen magance tashe tashen hankula a duniya, rahoton ya nuna cewa, tashe tashen hankula da aka fuskanta a sassan duniya sun haddasa mummunan hasarar makudan kudade, sai dai ya yi nuni da irin matakan da ya dace a bi wajen rigakafin tashe tashen hankula a duniyar.

Baya ga jefa rayuwar al'ummomi masu yawa cikin halin matsin rayuwa, tashe-tashen hankulan sun kuma yi sanadiyyar tafka hasarar makudan kudade, kamar yadda rahoton ya nuna. Bugu da kari rahoton ya nuna cewa, idan za'a iya daukar matakan rigakafin tashe tashen hankula a duniya, to za'a iya ajiye zunzurutun kudi da ya kai daga dalar Amurka biliyan 5 zuwa biliyan 70 a duk shekara.

Hanyoyin samar da zaman lafiya su ne binciken hadin gwiwa irinsa na farko da aka gudanar tsakanin MDD da bankin duniyar game da matakan da za su magance tashe tashen hankula. Rahoton ya zayyana hanyoyi masu yawa wadanda su ne ke haddadsa tashe tashen hankula a duniya da suka hada da tauyewa daidaikun jama'a harkokinsu na hana su damar yin wani tasiri a harkokin da suka shafi al'umma, ko kuma hana su damar amfanuwa daga dunbun albarkatun da Allah ya huwace musu, ko kuma rashin yi musu adalci, ko rashin ba su tsaro.

A cewar rahoton, ya kamata a tsara wasu shirye-shirye da kuma wasu dabaru da za su kasance a matsayin ginshiki wajen yin rigakafin tashe tashen hankula, rahoton ya kara da cewa, idan har aka samu barazanar barkewar tashin hankali mafi tsanani, yin amfani da hanyoyin tattaunawar sulhu shi ne kadai mafita da za ta warware matsalolin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China