Madam Kristalina Georgieva ta yaba sosai da garambawul din da kasar Sin ta yi ga sha'anin kudi, inda ta ce, cibiyoyin hada-hadar kudi masu inganci za su taimaka ga bunkasa kamfanoni da masana'antu.
A waje daya kuma, madam Georgieva ta ce, gwamnatin kasar Sin ta dade tana bude kofarta ga kasashen waje, abun da ya sa kasar Sin za ta kara shiga cikin takarar kasa da kasa a fannin tattalin arziki.(Murtala Zhang)