in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan Kim Jim-Yong da ya sake darewa kujerar shugaban bankin duniya
2016-09-01 13:38:23 cri
Ma'aikatar harkokin kudin kasar Sin ta fidda labari a daren jiya Laraba cewa, kasar Sin tana goyon bayan Kim Jim-Yong da ya sake hawa kujerar shugabacin bankin duniya.

A matsayin shugaba na yanzu na bankin duniya, za a kawo karshen wa'adin aikinsa a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017, shi ya sa, kwanan baya, Kim Jim-Yong ya gabatar da takardar neman ci gaba kan wannan aiki, sa'an nan, kwamitin manyan shugabannin zartaswa na bankin duniya ya kira wani taro domin tattaunawa kan harkokin zaben sabon shugaban bankin, inda ya kuma sanar da fara gabatar da 'yan takara a ranar 25 ga watan Agusta na bana, haka kuma, ya bukaci a gabatar da sunayen 'yan takara kafin karfe 6 na daren ranar 14 ga watan Satumba, bisa agogon yankin gabashin kasar Amurka.

Dangane da wannan lamari, ma'aikatar harkokin kudin kasar Sin ta bayyana cewa, bankin duniya shi ne muhimmiyar hukumar raya tattalin arziki ta kasa da kasa, kullum yana goyon bayan kasashen duniya wajen kawar da talauci da kuma inganta yunkurin ci gaban duniya, kasar Sin tana goyon bayan bankin duniya da ya zabi sabon shugabansa bisa ka'idojin ba tare da boye komai ba, da kuma zaben wanda ya fi dacewa da mukamin.

Bugu da kari, ma'aikatar harkokin kudin kasar Sin ta nuna cewa, kasar Sin ta nuna yabo ga Kim Jim-Yong game da babbar gudummawar da ya bayar a lokacin da yake shugabancin bankin duniya, shi ya sa, kasar Sin tana goyon bayan shi wajen cimma nasarar sake hawa kujerar shugaban bankin duniya.

Haka zalika, kasar Sin tana fatan bankin duniya zai ba da karin taimako wajen raya kasa da kasa, musamman ma wajen ba da gudummawa kan harkokin kawar da talauci, inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China