in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kudin Sin ya halarci taron ministocin kwamitin bunkasuwa karo na 94
2016-10-09 13:35:19 cri
Bankin duniya da Asusun ba da lamuni na IMF sun kira taron ministoci na kwamitin bunkasuwa karo na 94 a ranar 8 ga watan nan da muke ciki a babban birnin kasar Amurka, Washington DC, inda ministan harkokin kudin kasar Sin Lou Jiwei ya halarci wannan taro da kuma ba da wani jawabi.

A yayin dake ba da jawabi, Lou Jiwei ya bayyana cewa, ya kamata bankin duniya ya kyautata kwarewarsa wajen gudanar da ayyukansa da abin ya shafa, sa'an nan, ya karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsa da kasashe masu tasowa, domin baiwa kasashen goyon baya wajen raya tattalin arzikinsu.

Kaza lika, ya jaddada cewa, ya kamata a tsara ka'idojin rarraba jarin bankin farfado da raya kasashen duniya wanda yake karkashin bankin duniya bisa kudurin kyautata ikon jari da ikon kada kuri'u na kasashe masu tasowa dake cikin wannan banki, domin kasashen za su kara ikonsu na ba da shawara da na wakilci, ta yadda za a nuna kawo sauyin yanayin tattalin arziki na duniya yadda ya kamata, sa'an nan, za a iya kyautata tsarin gudanar da ayyukanmu bisa dokokin da abin ya shafa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China