in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fara sayar da man fetur da aka yi alkawarin za a samu a hukunce
2018-03-26 13:55:45 cri

Da karfe 9 na safiyar yau Litinin, kasar Sin ta fara sayar da man fetur da aka yi alkawarin za a samar a hukunce, a cibiyar cinikin makamashin kasa da kasa ta Shanghai, wato reshen kamfanin cinikin kayayyakin da aka yi alkawarin za a samar a Shanghai.

Rahotanni na cewa, man fetur da aka yi alkawarin za a samar shi ne hajar ta farko da kasar Sin ta fara sayar da ita cikin kasa da kasa, wadda aka yi ciniki da lissafin riba da kuma kammala cinikayya da kudin Sin wato RMB. Haka kuma, ana gudanar da ayyukan tunkarar kalubalen da ka iya kunno kai da kuma sa ido kan kasuwanni bisa ka'idojin kasa da kasa.

Shugaban kwamitin kula da harkokin hada-hadar kudi na kasar Sin Liu Shiyu ya halarci bikin bayyana farashin man fetur din, inda ya bayyana cewa, kwamitin yana da imani da kuma karfi wajen gina kasuwar man fetur da aka yi alkawarin za a samar da kyau, ta yadda wannan kasuwa za ta ba da gudummawa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China