in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta fahimci yarjejeniyar kasuwancin bai daya ba
2018-03-22 09:41:41 cri

A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ciniki marar shinge ta kasashen Afrika ba wato (AfCFTA), inda ta ba da hujjar cewa, har yanzu tana ci gaba da yin nazari kan wannan batu.

Yarjejeniyar ta AfCFTA, an kafa ta ne da nufin mayar da tsarin cikini na bai daya a tsakanin kasashen Afrika domin gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen cikin 'yanci.

Gwamnatin Najeriyar ta ce, ta kafa wani kwamiti da zai ci gaba da yin nazari game da bukatar kafa wannan yarjejeniyar ciniki marar shinge ta Afrika, kuma ana sa ran zai fitar da sakamakon da ya tattara nan da makonni biyu.

Kimanin kasashen Afrika 44 ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Laraba don kafa tsarin na AfCFTA a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a lokacin taron kolin kungiyar ta AU karo na 10 game da batun kafa tsarin cinikin na AfCFTA. A cewar kungiyar ta AU, shugabannin kasashen Afrika 19 ne suka halarci taron kolin.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya bai halarci taron kolin na Kigali ba.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Femi Adesina ya bayyana cewa, shugaba Buhari ba zai taba amincewa da duk wani abu da zai kawo nakasu ga ci gaba kananan masana'un cikin gidan kasar ba, wanda ake ganin alamun yarjejeniyar za ta iya haddasa hakan.

Adesina ya ce, shugaban Najeriyar yana da ra'ayin cewa, yarjejeniyar za ta iya kawo tarnaki wajen hana amfani da kayayyakin da kasar ke samarwa a cikin gida wanda kuma hakan ya ci karo da burin da kasar ke da shi.

Najeriya ita ce kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, kana kasa mafi karfin tattalin arziki a fadin nahiyar.

Kakakin fadar shugaban kasar ya ce, har yanzu Najeriyar ba ta da cikakkiyar masaniya game da yadda tasirin wannan yarjejeniyar ke da shi ga fannin tattalin arziki da tsaron kasar, don haka ne ma take ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin lalibo bakin zaren.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China