in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika za ta amfana da tsarin ciniki maras shinge a nahiyar duk da cewa akwai kalubaloli
2018-03-15 13:21:00 cri

Wani jami'in kasar Rwanda ya bayyana cewa, shirin kasuwanci maras shinge tsakanin kasashen nahiyar Afrika wato (AfCFTA) wanda ake yunkurin kafawa, zai amfanarwa Afrikar ta hanyoyin bunkasuwar cinikayya da masana'antu, duk da cewa akwai wasu kalubaloli dake tattare da gudanar da shirin.

Ana sa ran idan aka kaddamar da shirin na AfCFTA, zai rubanya adadin cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar nan da shekarar 2022, ministan ciniki da masana'antu na kasar Rwandan, Vincent Munyeshyaka shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua.

Tsarin AfCFTA zai rage tsadar kudaden gudanar da hada hadar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika, zai samar da damammakin kasuwanci, da habaka masana'antu, kana zai kuma kara adadin kayayyakin da ake samarwa a Afrikan.

An shirya gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afrika (AU) game da batun shirin na AfCFTA a Kigali a ranakun 17 zuwa 21 ga watan nan na Maris, inda ake sa ran shugabannin kasashen Afrika 55 za su halarta domin rattaba hannu kan yarjejeniyar ta AfCFTA.

Munyeshyaka ya lura cewa, shirin na ciniki maras shinge zai samar da damammakin ayyukan yi da rage zaman kashe wando, kuma zai ba da gagarumar gudunmowa ga shirin samar da dawwamamman ci gaban nahiyar da kuma kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummun kasashen na Afrika.

Ya ce, an tsara shirin na AfCFTA ne domin janyo hankulan masu zuba jari daga sassan duniya, da kuma taimakawa ci gaban Afrika wajen tsayawa da kafafunta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China