in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Shirin samar da yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka zai taimaki nahiyar wajen tafiya da zamani
2018-03-19 19:44:33 cri
Sakatariya mai wakiltar MDD, kuma mataimakiyar babban sakataren majalissar a hukumar dake lura da tattalin arzikin nahiyar Afirka Vera Songwe, ta bayyana manufar kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar ko AfCFTA a takaice, a matsayin manufar da za ta taimaki nahiyar wajen tunkarar sauye sauye da kasashen duniya masu wadata ke samu, tare da bunkasa tsarin cinikayya na kasa da kasa.

Vera Songwe, wadda ke bayyana hakan yau Litinin a birnin Kigalin kasar Rwanda, ta ce ana ci gaba da samun shingaye ga kasuwanni a sassan duniya daban daban, matakin da ka iya shafar Afirka, amma manufar AfCFTA ta zamo wani ginshiki na daidaita tsarin Afirka, don shiga a dama da ita a hada hadar cinikayya a yankin da take, tare da share mata fagen samun ci gaba mai dorewa.

Jami'ar ta kara da cewa, Afirka na da damar samun bunkasa, idan har kasashen nahiyar suka yi hadin gwiwa, maimakon daukar matakai na daidaikun kasashe. A cewar ta, yayin da ake fuskantar hali na rashin tabbas a kasuwannin duniya, ya dace nahiyar Afirka ta hada kai wajen duba irin na ta damammakin cimma nasara na bai daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China