in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na fatan samun cin moriyar juna ta shirin ciniki marar shinge
2018-03-22 10:00:04 cri

Shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasashen Afrika na sa ran za su ci moriyar juna karkashin shirin yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tsakanin kasashen nahiyar wato (AfCFTA).

Yarjejeniyar ta AfCFTA, za ta fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasasahen Afrika da sauran abokan huldarsu, Kagame ya bayyana hakan ne a taron kolin AU karo na 10 game da batun yarjejeniyar ta AfCFTA.

Idan aka tabbatar da kafuwar tsarin kasuwanci marar shinge a tsakanin kasashen na Afrika, bangarorin Afrikan da abokan huldarsu za su samar da wata babbar kasuwa mafi girma, kuma za ta amfanawa dukkanin bangarorin, in ji shugaban na Ruwanda.

Shugaban jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya bayyana cewa, tun kafin wannan lokacin, abokan huldar kasashen Afrika na ketare kamar kasar Sin da sauran kasashe, suna da kyakyyawar hulda tsakaninsu da Afrika.

Shugaba Issoufou ya kara da cewa, kasashen Afrika da sauran abokan huldarsu na kasashen duniya za su iya ci gaba da yin aiki tare karkashin shirin yarjejeniyar ta AfCTFA, ya kara da cewa, Afrika ne ya fi cancanta ta mayar da hankali wajen rungumar alfanun da tsarin na AfCFTA zai kawo game da ci gaba tare da hadin gwiwar abokan huldarsu na kasashen ketare, musamman ma kasar Sin.

Kasashen Afrika 44 ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Laraba da nufin kafa tsarin kasuwanci cikin 'yanci na AfCFTA a lokacin taron kolin na wuni guda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China