Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fada cikin wata sanarwa inda ta bayyana harin a matsayin ayyukan 'yan ta'adda, inda ta jaddada goyon bayan kasar Sudan ga kasar Masar wajen yakar ayyukan ta'addanci.
Ma'aikatar harkokin wajen ta mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Masar da al'ummar kasar da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da yin fatar samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata a harin.
Ma'aikatar ta kuma jaddada cikakken goyon bayan Sudan ga gwamnatin kasar ta Masar game da dukkan matakan da za ta dauka domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'ummar kasar daga fuskanta dukkan nau'ikan ayyukan ta'addanci da na bata gari. (Ahmad Fagam)