Kakakin SPLM tsagin arewaci, Mubarak Ardol, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, gwamnatin kasar ta sake saba yarjejeniyar tsagaita bude wutar inda ta afkawa magoya bayan kungiyar 'yan tawayen a jihar Blue Nile.
Ardol ya bayyana cewa, mayakan 'yan tawayen sun dakile wasu hare haren da dakarun gwamnatin Sudan suka kaddamar kansu a safiyar Asabar din da ta gabata inda suka shafe tsawon sa'a guda suna gwabzawa da dakarun gwamnatin a yankin Al-Rum dake jihar ta Blue Nile.
Sai dai kawo yanzu dakarun sojin kasar Sudan din ba su mayar da martani ba game da ikirarin da 'yan tawayen suka yi.
Mayakan SPLM/ tsagin arewaci sun jima suna arangama da dakarun gwamnatin Khartoum a kudancin jihohin Kordofan da Blue Nile tun a shekarar 2011, duk da yarjejeniyar shirin tsagaita bude wutar da aka kulla a lokuta da dama tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)