SUNA ya ruwaito cewa Shugaban Al-Bashir na jagorantar wakilan kasarsa zuwa taron na AU da aka amince da gudanar da shi yayin taron da Tarayyar ta yi a birnin Addis Ababa na Ethiopia cikin watan Junairun da ya gabata.
An fara taron ne a jiya Talata, inda za a kammala a yau Laraba.
Yankin ciniki mara shinge na nahiyar na da nufin zurfafa hadin kan tattalin arzikin nahiyar da inganta harkar noma da wadatar abinci da ayyukan masana'antu da sauya tsarin tattalin arziki ta hanyar samar da kasuwa ta bai daya da za ta ba da damar zirga-zirgar mutane da kayayyaki da jari da hidimomi ba tare da shinge ba.
Shugaban na Sudan ya samu rakiyar Ministan dake kula da fadarsa da Ministan harkokin wajen kasar da babban manajan ofishin shugaban kasa. (Fa'iza Mustapha)