in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda za ta karbi bakuncin taron kasa da kasa kan yaki da cutar kanjamau
2018-03-25 13:16:07 cri

Wani babban jami'in kiwon lafiya ya sanar da cewa an zabi kasar Rwanda domin ta karbi bakuncin babban taron kasa da kasa kan batun yaki da cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki da sauran cutukan da ake daukarsu ta hanyar jima'i na Afrika a 2019, wato ICASA.

Rwanda ta kaddamar da fara shirye shiryen karbar bakuncin taron, wanda ake sa ran samun halartar mutane sama da 10,000, cikinsu har da wasu jami'an hukumomin gwamnati, da manazarta, da kuma wakilai daga jami'o'i da humukomi masu zaman kansu, kamar yadda Patrick Ndimubanzi, minista mai kula da lafiyar jama'a da lafiyar matakin farko da ke cikin ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Rwanda ya tabbatar da hakan.

Taron dai zai tattauna ne game da dabarun da ya kamata a yi amfani da su wajen magance yaduwar cutar kanjamau a nahiyar Afrika, ya bayyana hakan ne a a taron manema labarai a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Rwanda za ta shirya taron, tare da hadin gwiwar kungiyar yaki da cutar kanjamau ta Afrika, wadda wasu masana ilmin kimiyya na Afirka da masu rajin yaki da cutar suka kafa ta a shekarar 1989. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China