in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na iya cimma burin kawar da kamuwa da cutar HIV a shekarar 2030
2016-06-11 13:25:15 cri
Ministan kiwon lafiya na kasar Zambiya Joseph Kasonde na ganin cewa mai yiyuwa ne ga Afrika ta kai ga cimma burin kawar da kamuwa da cutar kanjamau a shekarar 2030, da ma kawar da mace macen dake nasaba da Sida.

Mista Kasonde ya bayyana a kwanan nan cewa sabon adadin kamuwa ya ragu ko ma ya daidaita a yawancin kasashen Afrika a yayin da mace macen dake nasaba da cutar Sida suka yi kasa dalilin fadadar tsare tsaren bada jinya.

Da yake magana a matsayinsa na shugaban Gungun Afrika dake MDD a yayin wani taron manyan jami'ai na babban taron MDD kan karshen Sida da kuma Sida a birnin New York, ministan Zambiya na bayyana cewa mambobi 54 na Gungun Afrika na ganin cewa za'a iya cimma maradu dalilin niyyar siyasa da gwamnatocin kasashe suka nuna.

Duk da wadannan cigaba, har yanzu akwai sauran aiki. A game da mutane miliyan 2.1 da suka kamu da Sida a shekarar 2015, wanda kuma kashi 1 cikin 3 suna Afrika, da har yanzu ta zama cibiyar HIV.

Muna rike da wannan cikin fargaba game da raunin matasa cikin dogon lokaci, musamman ma 'yan mata wajen kamuwa da cutar Sida a Afrika, a cewar wata sanarwa da tawagar dindindin ta kasar Zambiya dake MDD ta fitar.

Ministan Zambiya ya bayyana cewa Gungun Afrika ya nuna yabo da cewa miliyan 15 na 'yan Afrika dake rayuwa tare da HIV na samun jinya game da cutar. Talauci da zaman kashe wando sun kara janyo tsanantar HIV/SIDA, a cewar jami'in.

Ya bayyana cewa wani aikin musamman ya kasance wajibi ga dukkan bangarori domin yaki da munanan sakamakon HIV/SIDA.

Taron da shugaban babban taron mista Mogens Lykketoft ya kira, ya amince da sanarwar siyasa kan hanya mafi sauri domin gaggauta yaki da Sida da kawo karshen annobar Sida a shekarar 2030. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China