in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika sun kara daura damarar yaki da cutar kanjamau
2017-12-02 13:22:45 cri
Yayin da aka yi bikin ranar yaki da cutar kanjamau a jiya, kasashen Afrika sun sake zage damtse na ganin sun kawar da cutar a tsakanin al'umma. Inda kasar Afrika ta kudu ta ce nan da shekarar 2020, za ta yi wa mutane miliyan 6.2 gwajin cutar kanjamau tare da ba su magani.

Yayin wani taro domin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya da aka yi a gabashin lardin Cape, Mataimakin shugaban Kasar Cyril Ramaphosa, ya ce kasar da ta fi kowacce a duniya yawan masu dauke da cutar kanjamau, ta yi niyyar yi wa mutane miliyan 6.2 gwaji tare da ba su magani nan zuwa shekarar 2020.

Afrika ta kudu, wadda aka yi kiyasin a bara kadai, mutane 270,000 ne suka kamu da cutar, na son rage adadin da ba zai dara 88,000 ba, ya zuwa shekarar 2020.

A Ghana kuwa, hukumar yaki da cutar kanjamau ta MDD ta ce an samu karuwar wadanda ke kamuwa da cutar da kaso 18 cikin 100 a bara, duk kuwa da nasarorin da aka samu na fatattakarta.

Daraktar hukumar a Ghana Angela Trenton-Mbonde, ta jadadda bukatar masu ruwa da tsaki da sauran abokan hulda su yi aiki tare wajen kirkiro sabbin hanyoyi samun nasarar kawar da cutar baki daya.

kasar Burundi a nata bangare, ta samu gagarumar nasara a fanni rage yaduwar cutar daga uwa zuwa da. Inda jami'ar ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Felicite Nkunzimana ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yada cutar daga uwa zuwa da a lokacin juna biyu ko haihuwa, ya ragu daga kaso 21 a shekarar 2012 zuwa kaso 6 a karshen bara.

A kasar Rwanda kuma, domin bikin ranar ta yaki da cutar, an kaddamar da wani sabon abun gwajin cutar kanjamau da mutane za su iya amfani da shi da kansu, inda ake sa ran zai kara yawan masu son yin gwaji bisa radin kansu, a wani yunkuri shawo kan annobar cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China