in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da sabon maganin cutar Sida a yayin taron yaki da cutar na kasa da kasa na bana
2016-07-20 11:00:26 cri

A jiya ne yayin taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa na shekarar 2016 da ke gudana yanzu haka a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu, aka gabatar da wasu sabbin nazarce-nazarce wadanda za su kai ga hada sabbin magungunan hana kamuwa da cutar.

Mahalarta taron, sun yi maraba da sabbin ci gaban da aka samu, a kokarin da ake na ganin bayan wannan cuta da ke lakume rayukan jama'a a sassa daban-daban na duniya.

Mataimakiyar darekta a cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Desmond Tutu da ke birnin Cape Town, kana shugabar kungiyar masu yaki da cutar AIDS ta kasa da kasa, Linda-Gail Bekker ta ce, a baya dai maganin yana rage yawan masu kamuwa da cutar ce kadai, amma sabon maganin zai kara karfin garkuwar dan-Adam na yakar cutar baki daya.

Shi ma babban mai binciken magungunan cutar ta kanjamau Larry Corey, ya ce, abin farin ciki ne ganin yadda magungunan da aka hada musamman domin kasar Afirka ta kudu, za a iya gwada su a sauran sassan duniya.

Shi dai nau'in maganin na HVTN 702 na gwaji ne, kafin a samu lasisin fara amfani da maganin a kasar Afirka ta kudu, kuma shi ne maganin hana kamuwa da cutar AIDS na farko da aka bullo da shi a duniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China