in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daraktan shirin UNAIDS ya bayyana damuwa game da yaduwar cutar Kanjamau a Angola
2017-10-06 12:47:02 cri
Daraktan Shirin yaki da cutar kanjamau na MDD a Angola Michel Kouakou, ya ce adadin yaduwar cutar kajamau da kashi 2.4 cikin dari a Angola abun damuwa ne, duk kuwa da kokarin da Gwamnatin kasar ke yi.

Da yake ganawa da manema labarai a wani bangare na taron karawa juna sani dake da nufin karfafa tsarin kiwon lafiyar al'umma a kasar, Michel Kouakou ya ce ayyukan shirin za su ci gaba da mayar da hankali wajen taimakawa Gwamnati daukar matakan yaki da cutar.

Ya ce shirin UNAIDS ya kasance ya na taimakawa Gwamnati aiwatar da shirin da aka yi wa lakabi da 'gwaji da magani' da aka kaddamar a watan Yunin da ya gabata domin dukkan masu dauke da cutar.

Ya ce manufar ita ce, daga nan zuwa 2030, shirin ya kai ga kaso 90 cikin dari na mutanen da ke dauke da cutar kanjamau wadanda ke karbar magani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China