in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana a Afirka za su gana game da bincike kan tasirin gwajin magungunan cutar HIV a Namibia
2016-09-08 09:37:08 cri

Masana da masu ruwa da tsaki sama da 120 daga kasashen nahiyar Afirka 11, za su gudanar da wani taro na kwanaki 4, domin nazartar tasirin gwaje gwajen da ake yiwa masu shan magungunan yaki da cutar HIV ko Sida a kasar Namibia. Wannan dai taro shi ne irin sa na farko da ya wakana a Namibia.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ce dai ta bayyana muhimmnacin tsarin gwajin magungunan cutar ta HIV wanda aka yiwa lakabi da ART.

Yayin taron na wannan karo wanda za a bude a ranar 13 ga watan nan na Satumba, masanan za su kara wa juna sani game da kwarewa da dabarun da kasashe daban daban ke bi, wajen gudanar da gwaji da kuma tasirin sakamakon da ake samu wajen jiyyar masu dauke da wannan cuta.

Masana dai na cewa, hanyar ART na da matukar muhimmanci wajen gano tasirin jiyyar da ake baiwa masu fama da cutar HIV, wanda hakan ke kai su ga ko dai samun sauki, ko kuma rasa rayukan su.

Kasar Namibia dai na cikin kasashe uku da ke kan gaba a nahiyar Afirka, a yawan masu fama da cutar HIV dake bukatar wannan gwaji na ART.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China