in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsaya kan wasu batutuwa a Somaliya
2018-02-12 10:10:44 cri

Shugabannin siyasar kasar Somaliya sun karkare taron wuni hudu da suka shirya a Mogadishu, inda suka cimma matsaya game da shawo kan wasu dunbun matsaloli da suka shafi batun tsaron kasar, da shirya tsarin siyasar kasar nan da shekarar 2020, da kuma batun rabon arzikin kasar.

Shugabannin sun kunshi na matakan gwamnatin tsakiya da gwamnatin shiyya, inda suka amince za su hanzarta tafiyar da ci gaban kasar da kuma horas da dakarun tsaro na musamman na Danab dake karkashin rundunar sojin kasar Somaliya domin taimakawa kasar wajen samun dawwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a karshen taron, gwamnati ta amince za'a tallafawa jami'an 'yan sandan shiyya, kana za'a samar da tallafin makamai ga jami'an tsaro na farin kaya, da ba su horo, da kayan aikin.

Taron ya umarci kwamitin tabbatar da tsaron kasar da ya samar da kasafin kudi wanda za'a samar da kudaden da za'a biya jami'an tsaro na shiyyoyin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China