in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 18 suka rasa rayuka sanadin harin bom a Mogadishu
2018-02-24 10:18:28 cri

Jiya Jumma'a aka kai hare-haren bama-bamai cikin motoci sau biyu a Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya, daya daga ciki, an kai harin ne a wurin dake kusa da fadar shugaban kasar, an ce, yayin hare-haren, a kalla mutane 18 suka rasa rayukansu, kana saura guda 20 suka ji rauni.

Bisa labarin da hukumar tsaron kasar ta bayar, an ce, a yammacin wannan ranar, da misalin karfe 6, bom ya fashe a cikin wata motar dake kusa da hedkwatar hukumar leken asiri da tsaron kasar ta Somaliya, bayan mintoci kusan 15, an tarwatsa bam da aka ajiye a cikin wata mota kan titin dake kusa da fadar shugaban kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China