in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia ta karbi iko da harkokin sufurin jiragen saman kasar bayan shekaru 27
2017-12-29 09:57:04 cri

Gwamnatin Somalia ta sanar a hukumance, da karbar iko da kula da sufurin jiragen samanta, bayan ya shafe shekaru 27 a hannun ofishin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya ICAO dake Nairobi.

Shugaban kasar Mohammed Abdullahi Farmajo ne ya kaddamar da ofisoshi da kayayyakin aiki da aka sanya a filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Mogadishu, yana mai bayyana wannan yunkuri a matsayin muhimmin mataki na samun ci gaban kasar.

Ya ce, al'amari ne mai daraja a gare su, ganin wannan rana mai cike da tarihi da suka karbi iko da kula da sufurin jiragen samansu, yana mai cewa, ba abu ne da ake same shi cikin sauki da sa'a ba, illa ta hanyar aiki tukuru.

Ya kuma godewa jami'an ma'aikatar sufuri da jiragen sama ta kasar da hukumar ICAO bisa kokarinsu na gudanar da aikin filin jirgin saman. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China