in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada kudurinta na mara baya ga warware rikicin siyasar Libya
2018-02-21 12:32:53 cri
Mukaddashin Jakadan kasar Sin a Libya Wang Qimin, ya jadadda kudurin kasarsa na ganin an warware rikicin siyasar Libya.

Wang Qimin ya bayyana haka ne a jiya Talata, yayin wani taron manema labarai da ya gudana bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Mohammed Sayala a birnin Tripoli.

Jami'in ya kuma jaddada muhimmincin zabukan kasar dake karatowa, wanda ya ce zai tabbatar da kammaluwar matakin mika mulki a kasar da rikici da dai-daita.

Ya kuma bayyana fatan samun ingantuwar yanayi a kasar, ta yadda ofishin jakadancin kasar Sin zai koma aiki a Tripoli, tare da ganin kamfanonin kasar Sin sun kammala ayyukanku da suke yi a kasar, wadanda aka dakatar tun shekarar 2011.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Libya Mohammed Sayala, ya amince da gayyatar da aka yi masa ta halartar taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da na kasashen Larabawa da zai gudana cikin watan Yuli a nan binin Beijing.

Ya kara da cewa, shi ma Firaminstan kasar Fayez Serraj, ya amince da gayyatar da aka yi masa ta halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika FOCAC da zai gudana a watan Satumba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China