in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta nemi taimakon Sin wajen farfado da tattalin arzikinta da kuma warware rikicin siyasar kasar
2018-02-20 12:33:50 cri

Wakilin kasar Sin dake kula da al'amuran Libya ya gana da shugaban majalisar koli ta kasar Libyan inda suka tattauna a ranar Litinin game da batun rikicin kasar Libyan.

Wang Qimin, jami'i mai kula da harkokin jakadancin kasar Sin a Libya ya kai ziyarar aiki ne a Tripoli, kuma ita ce ziyara ta farko da wani babban jami'in kasar Sin ya kai tun bayan da kasar Sin ta janye jakadanta daga kasar Libya a shekarar 2014 sakamakon tashin hankalin da ya barke a kasar.

An shirya wata ganawar da jami'in zai yi da ministan harkokin wajen Libya Mohamed Sayala a yau Talata, bayan ganawar da jami'in ya yi da shugaban majalisar kolin kasar Abdurrahman Swehli a ranar Litinin.

Wang ya bayyana cewa, taron ganawar ya shafi batun nazari kan rikicin siyasar kasar ne, da kuma muhimmancin daftarin da MDD ta gabatar wanda ya kunshi matakan da za su taimaka wajen warware rikicin siyasar kasar Libyan ta hanyar yin kwaskwarima kan yarjejeniyar warware rikicin siyasar kasar, kuma wannan shi ne batu guda daya tilo da kasar Sin ta goyi bayansa wanda zai dunkule tsarin shugabancin kasar Libyan waje guda.

Swehli ya yaba da irin goyon bayan da kasar Sin ke bayarwa wajen warware rikicin siyasar kasar ta Libya, inda ya nanata aniyar majalisar ta bude kofa ga dukkan bangarorin kasar don hawa teburin sulhu da nufin samar da dauwamamman zaman lafiya a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China