in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya Merkel murnar sake zabarta shugabar gwamnatin Jamus
2018-03-15 08:56:29 cri

A jiya Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Angela Merkel na sake zabarta a matsayin shugabar gwamnatin Jamus a karo na 4.

A wasikar taya murnar da ya aike da ita, shugaba Xi ya ce, tun lokacin da aka kafa cikakken tsarin mu'amala tsakanin kasar Sin da Jamus a shekarar 2014, ake ci gaba da samun kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu, ana ci gaba da samun zuzzurfar mu'amala da kyakkyawar hadin gwiwa, da kuma alakar kut-da-kut tsakanin sassan biyu a kokarin da suke na kyautata sha'anin tafiyar da harkokin kasa da kasa da gamayyar dangantakar kasashen duniya yadda ya kamata.

Shugaban na Sin ya ce, yana ba da muhimmanci matuka wajen kara ciyar da danganatakar dake tsakanin Sin da Jamus gaba, kana a shirye yake ya yi aiki tare da Merkel wajen yin hadin gwiwa da bunkasa amintakar dake tsakaninsu, da kuma daga matsayin dangantakar dake tsakanin sassan biyu zuwa matsayin koli domin samun gagarumin ci gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China