Ya kara da cewa, tabbas ne jama'ar Rasha za su ci gaba da hada karfi a kokarin da suke yi na raya kasar su karkashin jagorancin shugaba Putin.
A nasa bangaren kuma, Putin ya sake taya shugaba Xi Jinping murnar sake cin zaben zama shugaban kasar Sin. A cewarsa, yadda majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yanke wannan shawara, ya bayyana goyon bayan da al'ummar kasar suka nuna masa, shawarar da kuma ya samu tsayayyen goyon baya daga kasar ta Rasha.(Lubabatu)