in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya Putin murnar lashe zaben shugaban kasar Rasha
2018-03-19 10:18:08 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa Vladimir Putin sakon taya murnar lashe zaben shugaban kasar Rasha.

A cikin sakon, shugaba Xi ya nuna cewa, jama'ar kasar Rasha sun hada kansu sosai tare da dukufa wajen farfado da kasarsu a 'yan shekarun nan da suka gabata, abun da ya sa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar suka samu manyan nasarori, baya ga yadda Rashar take taka muhimmiyar rawa a cikin lamuran duniya. An yi imanin cewa, tabbas Rasha za ta kara samun sabbin nasarori kan ci gabanta.

Xi ya kara da cewa, a halin yanzu, dangantakar abota da ke tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tana matsayi mafi kyau a tarihi, wadda ta zama abun koyi wajen kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa ta girmamawa juna da samun adalci da hadin kai don moriyar juna, a kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.

Bugu da kari, Xi ya ce, kasar Sin na son yin kokari tare da Rasha wajen ciyar da dangantakarsu zuwa wani sabon mataki, ta yadda za ta taimakawa ci gaban kasashen biyu, da kara azama ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da duniya baki daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China