in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabn Xi ya aike da sakon ta'aziyyar hadarin jirgin saman Bangladesh
2018-03-14 10:55:08 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya sakamakon hadarin jirgin saman kasar Bangladesh wanda ya yi hadari a kasar Nepal a ranar 12 ga wata, inda ya hallaka mutane 49, kana mutane 22 suka samu raunuka.

A sakon da ya aikewa shugaba Md. Abdul Hamid na Bangladesh da shugaba Bidya Devi Bhandari na Nepal, Xi ya nuna juyayi game da afkuwar hadarin da kuma irin hasarar rayukan da ya haddasa.

A rana guda kuma, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang, ya aike da sakon ta'aziyya ga takwarorinsa Sheikh Hasina na kasar Bangladesh da K.P. Sharma Oli na kasar Nepal.

Jirgin saman mallakar kamfanin jirgin sama na U.S.-Bangla Airlines, yana dauke da fasinjoji 71 ne a lokacin da ya yi hadarin, wato a daidai lokacin da yake sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Tribhuvan na Kathmandu, babban birnin kasar Nepal, inda nan take ya kama da wuta. Daga cikin fasinjoji 67 dake jirgin, 32 'yan kasar Bangladesh ne, 33 kuma 'yan kasar Nepal ne, sai kuma saura mutane biyu daga kasashen Sin da Maldives.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China