in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu shugabannin kasashen waje sun taya Xi Jinping murnar zama shugaban kasar Sin a karo na 2
2018-03-19 10:34:32 cri
Wasu shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun mika sako ga Xi Jinping bi da bi ne, inda suka taya shi murnar zama shugaban kasar Sin a karo na biyu.

Shugaban kungiyar AU a wannan karo kuma shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, Sin ta samu manyan nasarori, kuma an kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar, sannan martabarta ta karu a idon duniya baki daya.

A nasa bangaren, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce, shugaba Xi Jinping ya jajirce tare da jagorantar inganta dangantakar abota tsakanin gwamnatin kasar Sin da MDD, inda ya ce, majalisar na son kara yin hadin gwiwa da kasar wajen kiyaye zaman lafiya, da samun ci gaba mai dorewa, da amfanawa jama'ar duniya gaba daya.

Hakazalika, shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli da na kasar Kenya Uhuru Kenyatta da shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso da na Burundi Pierre Nkurunziza da na Chadi Idriss Deby da shugaban Mozambique Filipe Nyusi da sarkin kasar Lesotho Letsie III da kuma shugaban kasar Seychelles Danny Faure, dukkansu sun taya Xi Jinping murnar zama shugaban kasar Sin a karo na 2. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China