A daidai lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya a jiya Alhamis, iyayen sun yi tattaki cikin lumana, domin tunatarwa gwamnatin Nijeriya irin kaddarar da ta aukawa 'ya'yansu a ranar 19 ga watan da ya gabata, lokacin da Kungiyar Bokon Haram ta farwa kwalejin 'yan mata ta Dapchi tare da dauke a kalla 'yan mata 110.
Taken ranar a bana shi ne 'matsa kaimi don samun ci gaba'. Sai dai iyayen sun ce babu yuwar samun wata ci gaba a rayuwarsu, muddun 'ya'yansu ba su dawo nan kusa cikin koshin lafiya ba.
Hukumomin a garin na Dapchi sun dauko malamai a kalla 300, inda suke addu'a a kullum domin neman dawowar 'yan matan cikin koshin lafiya.
Dan majalisa mai wakiltar Dapchi da makotan garuruwa Goni Bukar, ya shaidawa majalisar wakilan kasar cewa, addu'ar ta musammam za ta ci gaba har zuwa lokacin da 'yan matan za su dawo. (Fa'iza Mustapha)