Kwamishinan 'yan sandan jihar Damian Chukwu, ya shaidawa manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar cewa, 'yan sandan na cikin shirin yaki da ta'addanci domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka tura yankuna daban daban.
Damian Chukwu wanda ya ce sama da 'yan sanda 500 ne ke aiki cikin shirin rundunar soji mai taken 'Operation Lafiya Dole', ya jadadda kudurin rundunar na yaki da ta'addanci.
Shi ma ofishin dake kula da harkokin jin kai na MDD, ya ce an kashe jami'an bada agaji 3, yayin da ta ayyana batar wata ma'aikaciyar jinya yayin harin na Rann da aka kai ranar 1 ga wannan wata.
Hukumar ta ce jami'an na aikin bada agaji ne ga 'yan gudun hijira sama da 50,000 da suka tserewa gidajensu saboda tashin hankalin da yanki ke fama da shi.
Har ila yau, Damian Chukwu ya ce an tura 'yan sanda makarantun gwamnati dake jihar domin inganta taro. (Fa'iza Mustapha)